Rundunar sojin saman Najeriya ta kai harin bam a maboyar shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, a jihar Zamfara a jiya Asabar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa sojojin sun afkawa da dama cikin yan bindigar, masu biyayya ga Turji.
Cikakken bayanin abin da ya faru na zuwa ne a lokacin da ake tsaka da fama da bala’in yan bindigar, kuma Daily Trust ta rawaito cewa an kashe ‘yan fashi da dama.
Shugaban ‘yan bindigar, wanda aka ce yana daya daga cikin yankunansa da ke dajin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi a Zamfara a lokacin da suka kai harin, ya gudu.
Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindiga da dama sun jikkata a harin da aka kai ta sama tare da kashe wasu da ba a tantance ba.
KARANTA ANAN: Dubban Mambobin APC Ne Suka Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar PDP A Kaduna
Rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun nuna cewa Turji na cikin wadanda abin ya shafa amma wata majiya ta ce da kyar ya tsere tare da wasu mutanensa.
A ‘yan makonnin da suka gabata sojojin sun kara kai farmaki kan ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya, inda suka fatattaki wasu da ba na gwamnati ba da ke barna a fadin kasar.
Turji wanda ke rike da wata babbar kungiyar ‘yan bindiga, na kan gaba wajen kai hare-hare a Zamfara da wasu sassan yankin Arewa maso Yamma.
Har yanzu dai hukumomin sojin kasar ba su bayar da wani karin haske a hukumance kan farmakin da suka kai a maboyar Turji ba.
A wani labarin kuma: Ya Kamata Yan Najeriya Su Ƙara Ƙaimi Wajen Zuba Jari A Harkar Noma – Okowa
Gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman ‘yan Deltan da su kara saka hannun jari a harkar noma.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa wannan a ganin gwamnan na a matsayin hanyar dakile matsalar karancin abinci a Najeriya da samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arziki ga al’umma.