Biyo bayan yawaitar Kashe-kashe da garkuwa da mutane dake faruwa a fadin jihar Kaduna, Shugaban ‘yan Sanda na kasa Muhammad Adamu ya bada sanarwar tsige Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kaduna Ahmad Abdurrahman.
Sanarwa ta bayyana cewar an maye gurbin shi da Aji Ali Janga, kuma sauyin ya fara nan take, a kokarin da rundunar ‘yan sanda ke yi na ganin tsaro ya dawo a jihar musamman yadda al’amura suka rincabe akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
A kwanakin baya dai Gwamnan jihar Kaduna El Rufa’i ya kai ziyara ga shugaban ‘yan Sanda na kasa inda suka shafe tsawon lokaci suna ganawa, masu nazarin al’amura na ganin tsige Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kaduna bai rasa nasaba da ziyarar da gwamna El Rufa’i ya kaiwa shugaban ‘yan Sandan kwanakin baya.
An dai fara samun takun saka a tsakanin Gwamnan jihar Kaduna da Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar tun bayan wani hari da kabilun kadara suka kaiwa Fulani a yankin karamar hukumar Kajuru, inda El Rufa’i ya bayyana cewar an kashe Fulani sama da 100 a wannan hari, yayin da Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ya musanta bayanan gwamnan inda yace mutane kasa da 20 ne aka kashe.