Gabanin gudanar da zaben fidda gwanin da ke tafe, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya mika fom din tsayawa takarar sa na jam’iyyar APC.
Kungiyar goyon bayan sa mai suna Progressive Project TPP da ke Abuja ne suka mika fom din a daren ranar Laraba.
Gambari Zai Gana Da Kungiyar ASUU, Yayin Da Dalibai Ke Ci gaba da Zanga-zanga
An gabatar da takardar ne a Sakatariyar jam’iyyar ta kasa da misalin karfe 9 na daren Laraba.
Shugaban kungiyar TPP, Sanata Kabiru Gaya da Sanata Muhammadu Bulkachuwa ne suka jagoranci kungiyar wadanda suka mika fom ga sakataren kungiyar APC na kasa, Alhaji Sulaiman Argungu a wani takaitaccen biki da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar.
Idan dai ba a manta ba a makon da ya gabata ne kungiyar ta karbi fom din takarar mataimakin shugaban kasa a cibiyar taron kasa da kasa da ke Abuja.
Bayan cigaban da aka samu ne kungiyar ta sha alwashin marawa mai neman tsayawa takarar shugaban kasa baya a jam’iyyar.
Jagoran jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu, shi ma ya mika nasa fom a ranar Laraba.