Tsohon gwamnan jihar Enugu, kuma Sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas, Chimaroke Nnamani, ya ce ya zabi ya yi yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu maimakon Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, saboda jam’iyya ta yi watsi da shiyya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Nnamani a wata sanarwa da ya fitar da kansa ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, ya ce babbar jam’iyyar adawa ta karya kundin tsarin mulkin ta, ta kuma hana kudancin kasar damar tsayawa takarar shugaban kasa, don haka ya yanke shawarar tsayawa Tinubu.
Sanatan, wanda kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya dakatar a kwanakin baya, ya bayyana cewa, shugaba Buhari bisa la’akari da yadda ake tafiyar da mulkin Arewa da Kudanci, ya samar da wata tagar daidaita siyasar da ta baiwa Tinubu damar fitowa takarar shugaban kasa, amma jam’iyyar PDP ta kasa yin hakan.
KU KARANTA KUMA Nan Bada Jimawa Ba Zan Yi Magana Akan Atiku Da Rikicin Jam’iyyar
Ya ce: “Saboda bukatar rabi da kuma karkatar da muhimman mukamai na siyasa a tsakanin al’ummar kasarmu daban-daban, kundin tsarin mulkin PDP ya bayyana karara cewa za ta yi aiki da tsarin karba-karba da shiyya-shiyya na jam’iyya da ofisoshin zabe na jama’a a kowane lokaci don bin ka’idar daidaito, adalci da gaskiya.
“Ko a lokacin da shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu ya tabbatar da cewa zai sauka daga mulki idan dan Arewa ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023, shugabanni sun yi watsi da tanadin kundin tsarin mulkin kasar, suka mayar da hankali kan son zuciyarsu.
“Mun tuna cewa PDP a 2019 ta baiwa Arewa damar tsayawa takarar shugaban kasa a Fatakwal, jihar Ribas inda Atiku Abubakar ya samu tikitin tsayawa takara.
“An yi tsammanin cewa a shekarar 2023, jam’iyyar PDP ta hanyar da ta dace ta baiwa Kudu damar tsayawa takara, amma jam’iyyar a matakin da ta dauka ta bude fafatawar ne ga ‘yan Arewa da Kudu.
“Sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa ya harzuka masu aminci na Kudancin PDP ciki har da Gwamnonin G.5 wadanda suka dage kan mutunta ka’idar karba-karba ta Arewa da Kudu .
“Sanata Nnamani ya ce matakin da PDP ta dauka ya yi daidai da rashin adalci da rashin daidato tare da tabbatar da cewa ba daidai ba ne a bar mulki a Arewa bayan mulkin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.”
A Wani Labarin Kuma Sabbin Kudi: Babban Bankin Kasa CBN Zai Sa Ido Kan Hada-Hadar Bankuna
Babban bankin Kasa (CBN) ya ce zai sanya ido a kan dakunan bayanan bankunan da ke jihar Ribas a matsayin hanyar da za ta binciko bankunan da ke tara sabbin takardun kudi na Naira da kuma wahalar da ‘yan Najeriya.
Shugaban CBN reshen Jihar Ribas, Mista Maxwell Okafor, ne ya bayyana haka a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, bayan da CBN ya yi musayar kudade a Fatakwal da Igwurita a karamar hukumar Ikwerre ta Jihar ranar Lahadi.