By Abbas Yakubu Yaura
Kasar Ekwador na fuskantar “mummunan barazana” daga masu safarar muggan kwayoyi wadanda ke son “karbe iko da dukkan gidajen yarin kasar,” in ji Shugaba Guillermo Lasso a ranar Litinin, bayan da shugabannin sojoji dana gidan yari suka yi murabus sakamakon tarzomar gidan yari data yi sanadin mutuwar mutane 68.
Lasso yace, ‘yan sanda da sojoji suna gudanar da wani gagarumin farmaki a gidan yari mai cunkoson jama’a a Guayaquil, inda aka kwashe kwanaki biyu ana gwabza fada tsakanin fursunonin dauke da bindigogi da adduna da bama-bamai da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Shugaban yace kasar tana fuskantar”daya daga cikin manyan rikice-rikice a cikin ‘yan shekarun nan” kuma ya yi gargadin cewa irin kwayoyin mafia “suna kawo rashin tsaro a titunanmu.sannan yace “Na yi alkawarin daukar matakin hadin gwiwa don kawo karshen kashe-kashen da ake yi a gidajen yarin kasar.
Sojoji dauke da bindigu sun shiga kewayen gidan yarin na Guayas 1, wanda ya hada da jami’an tsaro da dama, da rana, a cewar ‘yan jaridar AFP da ke wurin. Amma da yamma har yanzu basu shiga wuraren da fursunonin ke zaune ba, a cewar wata majiyar soja.
‘Yan sanda da sojoji 1,000 sun shiga Guayas 1 “don sarrafa hanyar shiga waje dana ciki”, in ji Lasso.
Lasso yana magana ne bayan amincewa da murabus din Vice Admiral Jorge Cabrera shugaban rundunar hadin gwiwa da Bolivar Garzon, shugaban hukumar kula da gidajen yari ta SNAI.
Shafukan sada zumunta sun nuna munanan hotunan fursunonin suna duka da kuma cinna wa gawarwakin da suka zubar da jini wuta a wata fashewa da gwamnati ta yi wa lakabi da “walau.”
Kakakin shugaban kasar Carlos Jijon ya shaida wa kafar sadarwa ta Teleamazonas cewa, ” kasar na fuskantar hare-hare, a karkashin wata kungiyar mafia ta kasa da kasa ta masu safarar miyagun kwayoyi.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Fiye da fursunoni 320 ne aka kashe ya zuwa yanzu a cikin 2021, kuma tarzomar ta baya-bayan nan ta faru duk da dokar ta-baci da aka sanya a gidan yarin Ecuador bayan wani kazamin fada a watan Satumba.
Sai dai Lasso ya ayyana dokar ta baci guda biyu bayan afkuwar tashin hankalin gidan yarin a watan Satumba – daya na gidajen yarin kasar da kuma wani na tara sojoji a kan tituna na tsawon kwanaki 60 domin tallafawa sojojin dake sintirin binciken kan laifuka.
Daga baya kotun tsarin mulkin kasar ta sanya iyaka kan tsoma bakin zartaswa, tare da hana sojoji shiga cikin gidajen yari tare da bada izinin tattara su a tsakanin fararen hula na tsawon kwanaki 30.
Kazalika A makon daya gabata ne, wani sabon na’urar nadar bayanai ta radar da Ecuador ta yi don duba shirye-shiryen jigilar muggan kwayoyi ta lalace sakamakon fashewar wani abu da gwamnati tace mai yiwuwa harin “yan ta’adda ne”.