Shugabannin kasashe da dama ne suka halartar taron don girmama gawar tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe da aka gudanar a ranar Asabar a filin wasan birnin Harare.
Daga cikin wadannan suka halarci wadannan addu’o’in sun hada na Kenya Uhuru Kenyatta, na Afirka ta Kudu Cyrl Ramaphosa, sai Denis Sassou Nguesso na Congo Brazzaville da kuma Obiang Nguema na Equatorial Guinea.
Haka zalika akwai tsoffin aminan shugaban da suka hada da Kenneth Kaunda na Zambia, Olusegun Obasanjo na Nijeriya da kuma Joaquin Chissano na Mozambique da suka halarci taron.
To sai dai bayan wadannan addu’o’i, har yanzu ba a bayyana ranar da za a rufe gawar tsohon shugaba Mugabe ba, wanda ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.