A karshen makon nan ne Ƙungiyar kakakin majalisun jihohi suka nuna goyon bayan su da a kafa rundunar yan sandar Jihohi don kawo karshen matsalolin tsaro dake addabar kasar nan.
Kazalika kungiyar ta bukaci a kafa rundunar yan sandar al’umma, wanda a cewar ta hakan shi ma zai taimaka matuƙa gaya.
Kungiyar wacce ta mika wannan bukata cikin wata takardar bayan taro da ya gudana a birnin Asaba na Jihar Delta wanda Shugaban ta kuma kakakin Majalisar dokokin jihar Bauchi Abubakar Suleiman ya jagoranta, ta ce lallai yanzu matsalar tsaro a kasar nan ta zama Allah Sarki.
A gefe guda kuma gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa ya bukaci zama teburin sulhu don samo bakin zaren warware rikicin Fifiko a shugabancin Kasar nan.
Ya ce kasar nan ta shiga wani hali da dole sai ta samu nagartattun shugabanni sa za su tsaya haikan wajen kare martabar yan kasa tare da haɗa kansu.