By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani, ya ce shugabannin tsaro a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba sa gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Tsohon dan majalisar ya yi magana ne a gidan talabijin na Arise TV kan tabarbarewar tsaro a kasar da kuma yadda ake ganin sakacin gwamnati na shawo kan lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Taya Kakakin Majalisar Wakilai, Gbajabiamila Murnar Cika Shekaru 60
Ya ce, “Matsalar da muke fuskanta, ita ce kawai yadda shugabannin tsaro ba sa gudanar da ayyukansu. Majalisa ba za ta iya korar su ba. Shugaban kasa ne ya kamata ya dauki nauyin hakan”.
“Misali, a shekarar da ta gabata, ‘yan bindiga sun kai hari a makarantar horas da sojoji ta Najeriya, kuma an yi garkuwa da soja daya ko biyu. Ba a kori kowa ba. Babu wanda aka azabtar. Babu wanda ya yi murabus. Kuma alhakin shugaban kasa ne ya dauki mataki.”
Ya ce majalisar dokokin kasar ta sha yin kira da a kori shugabannin jami’an tsaro ba tare da wata fa’ida ba.
“Sau da yawa a lokacin da muke majalisar dokokin kasar, mun yi kira da a kori shugabannin tsaro. Sai dai hoton da ake ta kitsawa a kasar a wancan lokaci shi ne cewa wadannan mutane suna yin abin da ya kamata a yi kuma matsalar ita ce Majalisar Dokoki ta kasa.
“Amma kuna iya ganin abin da ya faru a yau. Don haka muna bukatar mu samu shugaban kasa wanda a shirye yake ya wuce na cikin sa, fiye da shawarar mutanen da ba su fada masa gaskiya ba,” inji shi.
A wani labarin kuma Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Juma’a sun kai harin bam a ofishin ‘yan sanda da ke Eika-Ohizenyi a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi.
Yayin harin sun kashe wani dan sanda mai muƙamin wato sufeto Jibril da ke bakin aiki.
Wani mazaunin yankin, Malam Momoh Abubakar, ya bayyana cewa maharan sun mamaye ofishin jami’an ne da misalin karfe 12:15 na safe dauke da bama-bamai da sauran makamai.
Abubakar ya kara da cewa maharan sun samu sarari domin sun shafe sama da awanni biyu suna gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama daga jami’an tsaro ko jama’ar gari ba.
Mazaunin garin ya kara da cewa jami’in dan sanda daya tilo da ke bakin aiki, Jibril wanda aka fi sani da Yellow, ya mutu a harin yayin da motar da ke aiki a ofishin ‘yan sandan ta lalace.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun farfasa gilasan babban masallacin unguwar Eika da cocin Katolika da ke kusa da ofishin ‘yan sanda.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Edward Egbuka, ya ce ya ba da umarnin tura karin jami’an domin aiki, wadanda suka hada da jami’an rundunar ‘yan sandan ko ta kwana, dana sashin yaki da ta’addanci, sashen amsa kiran gaggawa, ofishin leken asiri na jihar tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin dawo da su.