Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Alkali Usman, ya tashi daga babban birnin tarayya Abuja, domin ziyartar inda ginin ya rufta a unguwar Ikoyi ta jihar Legas.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, wani babban dan sanda a jihar, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, da wasu manyan ‘yan sandan jihar na jiran tarbar IGP a filin jirgin sama da ke Ikeja.
“IGP din yana zuwa Legas ne domin ya ziyarci wurin da ginin ya rufta a Ikoyi. IGP din ya riga ya taso kuma yana iya sauka kowane lokaci daga yanzu,” inji majiyar.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta Ruwaito cewa, an gano gawarwakin mutane akalla 10 daga baraguzan ginin bene mai hawa 21 da ya ruguje a jiya Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar PRP ta Sanya Ranar Gudanar da Babban Taronta na Kasa
Wani da ya tsira daga lamarin Mai suna, Gabriel Bassey, ya ce kimanin mutane 50 ne suka makale a cikin baraguzan ginin da ya ruguje.
Har yanzu ana ci gaba da kokarin neman da ceto wasu daga cikin wadanda Lamarin ya rutsa da su.
Comments 1