Sijibomi Ogundele shi ne matashi ma fi karancin shekaru da Ubangiji ya daukaka a Najeriya a harkar sana’ar gidaje, Legit.ng ta ruwaito.
KURANTA: Yadda na yi cinikin biliyan 1 a shekarar 2022, ‘Yar Najeriya
Kamfaninsa, Sujimoto Construction shi ne daya cikin kamfanonin da ke harkokin gidaje da gine-gine mafi daukaka a Najeriya.
Labarin Sujimoto daya ne cikin labaran wadanda suka samu daukaka cikin kankanin lokaci wanda zai ba matasa da dama kwarin gwiwa.
Ya tashi ne a gidan da babu komai cikin matsanancin talauci inda ya dinga fama wurin yin fadi-tashi kala-kala.
An haife shi a shekarar 1981 a ranar 8 ga watan Afirilu, mahaifinsa, Samson Idowu Ogundele ma’aikaci ne, yayin da mahaifiyarsa, Sijibomi tana sana’o’inta a Agege.
Bayan ya tashi a Oko-Oba, inda mutane biyu ne kadai ke da injin samar da wutar lantarki, daga nan ne ya lashi takobin ba zai cigaba da zama cikin talauci ba, har sai da ya daukaka.
Ya je makarantar firamare a Oko-Oba, da kuma Ijebu-Ode tare da Kwalejin Jihar Legas, Meiran. Daga bisani ya bar Najeriya don karantu a fannin shari’a a Jami’ar Anglia Ruskin, da ke Ingila.
Saboda yawace-yawacensa, Sijibomi yana jin Hausa, Yoruba, Yaren Faransa, Spanish, da kuma Larabci da Japanese.
Yayin da yake taya mahaifiyarsa da sana’arta ta kasuwanci, yana tura kaya a baro daga wuri zuwa wuri. Sannan taya taya wasu ‘yan kasuwar kai kaya da baron inda suke biyan da kudade.
Daga nan ya cigaba da kananun sana’o’i kafin Ubangiji ya daukaka shi har ya fara sana’ar gidaje.
A shekarar 1998 ne ya fara harkar gidaje yayin da yake zama a Faransa ta kudu. Daga nan ba siya wani wuri a Paris, wanda ya yanke shawarar sauya fasalinsa.
Bayan gyara shi ne ya sayar da tare da samun riba. Bayan ya koma Najeriya a shekarar 2014 ne ya cigaba da sana’ar ta shi.
Ya samar da Sujimoto Group a Shekarau 2013 wacce ta kulla abota da Yazeed Alrahji da ke Saudiyya. Yanzu haka yana da ofisoshi a garin Legas, Abuja, Accra, Riyadh, Dubai, Madrid da Paris.
Kwamacala: Yadda Wani Uba Ya Sanya Hannun Da ‘Yarsa Kan Kwangilar Ba Ita Babu Kawance Da Namiji
Wani uba ya kwantar da hankalinsa ta hanyar yin Yarjejeniya da yarinyarsa wajen sanya hannu kan kwangilar da zai hana ta yin kwance da namiji har sai ta cika shekaru 20,Legit.ng ta rawaito.
Wani mai amfani da Facebook Emmanuel Stephen ya raba hoton mai kyau na mahaifi da ‘yarsa suna Yarjejeniyar sanya hannu a dokar.
A yayin da wasu iyayen suka so ra’ayin nasa, wasu kuma suka bar ra’ayin uban inda suka bayyana cewa akwai hanyoyi da yawa a kusa da wannan.