Majalisar Wakilan nTarayya ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya wato CBN Godwin Emfiele da kuma babban Hafsan Sojin Najeriya Manjo Janar Ibrahim Attahdiru da su zo su gurfana a gaban ta su yi bayani kan yadda aka sayi makamai.
Majalisar ta cimma wannan matsaya ne jim kadan bayan wani zama da kwamitin ta ya yi kan nazarin yadda aka sayhi makaman da yadda aka yi mafdna da su da kuma kayyaykin aikin tsaro.
Wannan mutane guda biyu da aka gayyata ana sa ran za su gurfana ne a gaban majalisar a ranar bakwai ga watan gobe.
Sauran wadanda aka gayyatan sun hada da Ma’aikatar Kudi da hukumar kididdiga da tsara siyan kayaykin gwamnati da Ma’aiktar tsaro da kuma Ma’aikatar Cikin gida.
Manjo Janar Attahiru ya tura wakilin shi Manjo Janar C. Ofuche a zaman majalisar da ya gabata to sai dai majalisar ta ce zuwa da kai ya fi sako.
Mambobin Kwamitin Majalisar sun ce wannan al’amari ne babba da ba ya bukatar aike, don haka dole Hafsan sojin ya gurfana da kan shi ya yi bayani.