Wata Matashiya ta bayyana irin yadda suka kwashi yan kallo ita da wani saurayi bayan da ta roke shi da ya rage mun hanya a mota, inda ya aike ta siya mishi Gasasshen Masara.
Matashiyar Mai Suna Winnie Wheeny a shafin Tuwita, ta wallafa cewa ta yi matuƙar nadamar shiga motar saurayin bayan da ya ce ladar shi ita ce kawai zai aiketa ta je siya siya mishi Gasasshen Masara.
“Ji gayen nan fah ya rage mun hanya a mota, muna zuwa sai na ga ya yi burki a bakin hanya ya cire kuɗi a Aljihun shi wai na je na siya mishi masara”
To sai dai mabiyan ta da dama sun yi ta tofa albarkacin bakinsu, inda wasu ke Fatan Allah Kara yayin da wasu kuma ke jajanta mata dangane da wannan bakon al’amari.
Wani mai suna @Kory_Babayope ya ce da ma nufin ki ya fita ya bar ki a cikin motar ne ya je siyan masarar da kan shi? Irin wannan tsaurin ido naki”
“Wasu na iya ɗaukar Kasada fah, to idan kika je kika gudu da masarar fah” Cewar @Wilson_ikpeme
Sai kuma wani mai suna @Jude_glory ta ce Allah Kara, gobe ma za ki nemi a rage miki hanya.
Mu kuma a nan za mu iya cewa idan da kwadayi ta tabbasa da akwai wulakanci, kazalika kowa ya hau motar kwadayi lallai babu inda za ta sauke shi sai tashar wulakanci.