Jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rashin jin dadinsa game yadda wasu suke murna da sauke Oshiomole a matsayin shugaban jam’iyyar na APC.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata takarda da ya rattabawa hannu ajiya Talata jim kadan bayan hukuncin Kotu game da Oshiomole.
“Wata dadaddiyar cuta ce ta bukatar 2023, wadda ta damu wasu ‘yan siyasa da kuma abokansu ‘yan jarida,” Tinubu ya bayyana a sanarwar.
A kwanakin baya rahotanni sun bayyana yadda kungiyar gwamnonin APC ta kira kwamitin gudanarwar jam’iyyar na kasa da ya sauke Oshiomole daga mukaminsa, inda suka goyi bayan hukuncin wata kotu a Abuja.
https://dimokuradiyya.com.ng/an-bawa-sirikin-ganduje-rikon-shugabancin-jamiyyar-apc-na-wucin-gadi/
Sai dai Oshionole ya daukaka kara a wata kotu dake Jihar Kano, wadda ta dakatar da aiwatar da hukuncin sauke shin.
Rashin jituwa tsakanin gwamnonin APC da kuma shugabancin jam’iyyar na kasa karkashin Adams Oshiomole ya janyo rabuwar kai a jam’iyyar.
Tinubu ya kara da cewa dole su girmama hukuncin kotu, amma a cewarsa dakatar da Oshiomole ba shi ne mafita ga ‘ya’yan jam’iyyar APC ba.
Jagoran jam’iyyar ya ce a halin da ake wasu bata garin jam’iyyar ne ke amfani da wata manufa ta kashin kansu wajen kawo hargitsi a tsakanin gwamnoni da kuma shugabancin jam’iyyar kamar yadda ta faru tsakanin Adams Oshiomole da kuma Godwin Obaseki.