Gwamnan jihar Edo Mista Godwin Obaseki ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC jim kadan bayan wata ganawarsa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin tarayya dake Villa a Abuja.
Ficewar tasa nada alaka da irin sabanin da suka dade suna samu da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Adams Oshiomole.
https://dimokuradiyya.com.ng/atiku-na-zawarcin-obaseki-ya-koma-jamiyyar-pdp/
Kuma na da alaka da rashin samun tikitin tsayawa takarar zaɓen fidda gwani da za a jihar, wanda kwamitin tantancewa na jam’iyyar APC suka ce bai cancanta ya tsaya saboda tuhumarsa da suke da badakala kan takardun makarantarsa.
Ana kyautata zabon cewa gwamna Obaseki nan bada jimawa ba zai bayyana komawarsa jam’iyyar PDP, wanda tun bayan rashin nasararsa ake ta tsammanin komawarsa inuwar jam’iyyar ta PDP.