Bashir Sanata daga jam’iyyar PDP tsagin Kwankwasiyya ya ce, jam’iyyar APC mai mulki kama karya kawai ta ke musamman a lokutan zaɓe wanda hakan ya nun cewa basa bin dokokin zaɓe a ƙasar nan.
Bashir Sanata ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na gidan rediyon Freedom dake Kano, yana mai cewa ko a zaɓen baya da ya gabata mutane sun tabbatar da irin yadda APC ke tafka rashin adalci a yayin zaɓe.
Ya ƙara da cewa irin wannan matsalar ce ke jefa wa masu dangwalen ƙuri’a tsoro wajen ƙauracewa zuwa wuraren zaɓuka domin kaucewa faɗawa cikin masu maguɗi.