Hadimin ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen shekara ta 2019 Injiniya Abba Kabir Yusif (Abba Gida-gida), Ibrahim Adam ya mayarwa da wani matashi martani game da iƙirarinsa na cewa duk yankin Arewa babu wani ɗan siyasa da yake gina rayuwar mabiyansa.
Ibraim Adam wanda hadimi ne ga Abba Gida-gida ya wallafa martanin ne a kafar sadarwa ta Facebook.
“Wato nayi mamaki da naga wani rubutu na son zuciya da wani bawan Allah yayi akan cewa a Arewa babu shugaba dake son ci gaban yaronsa na siyasa kamar Tinubu ba. Shi wannan marubucin ina ga ya manta da mutane irinsu kwankwaso da suka dɗaga yaronsu na siyasa daga ‘yan aike zuwa wasu manyan mutane”.
Kwankwaso ya taimaki mutane a duk muƙamin da ya samu na gwamna da kuma Ministan tsaro, kaɗan daga ciki sune:
ABDULLAHI UMAR GANDUJE: ya yi mataimakin gwamna daga shekara ta 1999 zuwa 2003. A 2003 ya zama hadimin ministan tsaro. A 2007 RMK ya kai shi wajen Yar’adua a masa Ambasada a ƙasar China, amma Allah bai nufa ba. A shekara ta 2008 an yi masa E.S na Lake Chad River Basin a ƙasar Chad Republic. A 20011 an dawo da shi kuma an bashi mataimakin gwamna. A shekara ta 2015 an ɗauki takara gwamna an bashi, kuma an yi masa yaƙin neman zaɓe babu har ya kai ga nasara.
–
HON. AHMAD GARBA BICHI: H.O.D ne a Fagge Local Government, kwankwaso ya ɗauko shi ya yi masa MD KASCO a 1999 – 2003 daga 2005 – 2007 Kwankwaso ya kai shi wajen Obasanjo aka yi masa E.S Hadejia Jama’are River Basin Development Authority, Sannan a 2007 aka ba shi takarar mataimakin gwamna lokacin da aka hana Kwankwaso yin akara, ya ɗauki takara gwamna gaba ɗaya ya ba shi. A 2007 aka ba shi Ministan kasuwanci da ma’aikatu.
– RABIU SULAIMAN BICHI:
Ma’aikaci ne a FCDA kafin Kwankwaso ya shigo da shi siyasa a 1999. RMK ya ba shi MD na KNUPDA a 1999, a 2002 RMK ya ba shi Kwamishina. A 2003, RMK ya kai shi wajen Obasanjo aka ba shi MD/CEO Infrastructure Bank of Nigeria (4 years) a 2008 RMK ya kai shi wajen Yar’adua aka ba shi Darakta na FCDA Board. A 2011 RMK ya ba shi SSG har 2015.
– BALA GWAGWARWA: Ya daɗe yana Gwagwarmaya a siyasa amma Allah bai sa zai zama wani abu ba sai dawowar shi gidan siyasar Madugu. Kwankwaso ya ba shi Kwamishina hukumar ruwa, sannan ya kara ba shi Kwamishina na Science and Technology. A 2013 da aka yi APC, Kwankwaso ya banƙara sai da aka bashi National Treasurer na ƙasa gaba ɗaya wanda sai 2018 ya sauka.
AMINU DABO: Abokin Kwankwaso ne tun a makaranta. A 1999 Kwankwaso Ya ba shi Kwamishina rna Land and Survey, a 2002 Kwankwaso Yaje ya dinga roƙar Obasanjo har sai da aka ba shi MD na Nigeria Port Authority.
HAFIZU ABUBAKAR: Lecturer ne a BUK kafin 1999 inda RMK ya ba shi S.A on Political Affairs, a 2000 aka ba shi Kwamishina na Finance. A 2003 aka ba shi S.A to the Minister of Defence, a 2011 aka babshi Head of Service amma yace a’a yana da buri ya zama Professor. A 2015 aka ɗauko shi aka ba shi takarar mataimakin gwamna har 2018.
AKILU SANI INDABAWA: S.A ne na Ministan tsaro 2003 – 2006. RMK ya zaɓe sa a matsayin shugaban matansa na Jam’iyyar PDPa Najeriya. Daga baya RMK ya kai shi wajen shugaban ƙasa Jonathan aka ba shi S.A na maitaimakin shugaban ƙasa akan harkokin siyasa.
BARR.FAROUK IYA: Yana Chamber shi yana aiki RMK ya ɗauko shi ya kai shi wajen Jonathan aka ba shi Board Member a NDDC (NIGER DELTA DEV. COMM). A 2009 aka ba shi Shugaban Jam’iyyar na PDP. A 2011 RMK ya ba shi Kwamishinan ilimi 2011 – 2014
Ibrahim ya kara da cewa “yanzu a cikin mutanen nan wane ne bai zama jigo ba a faɗin ƙasar nan a sanadiyyar Kwankwaso?.
Sai dai a cikin martanin nasa bai kama suna ba balle a ce ga da wanda yake.