Siyasa: Na goyi bayan matakin da kwamitin tantancewa suka dauka akan Obaseki – Cewar Ganduje.

Gwamnan Kano Dalta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ya goyi bayan soke takarar Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a karo na biyu.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a taron karin bayani dangane da halin da jihar ke ciki kan cutar sarke numfashi, Ganduje ya ce Kano za ta yi bakin duk wani kokarin da za ta yi domin ganin jam’iyyar su ta APC ta yi nasara a zaben, wanda za a gudanar cikin watan Satumba, 2020.

Don haka ya ce idan aka sake tsaida Obaseki, za a iya fuskantar rasa kujerar, ko da kuwa shi ne ya yi nasara, kamar abin da ya faru a Jihar Bayelsa.

APC ta hana Obaseki sake tsayawa takara sakamakon ruguntsimin rikicin sa da Shugaban APC na Kasa, Mista Adams Oshiomole.

Kwamitin Tantance ‘Yan Takara ya ki tsayar da Obaseki a bisa zargin ya na da matsala da takardun makarantarsa.

https://dimokuradiyya.com.ng/kano-za-ta-tallafa-wa-apc-domin-ta-lashe-zaben-gwamna-a-edo-ganduje/

A madadin Obaseki, Oshiomhole ya dauko Eze Iyamu, a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na zaben gwamnan jihar Edo

Idan ba a manta ba, Oshiomhole ya rika kiran Iyamu mutumin da bai kamata a damka wa amana ba, a lokacin da Iyamu ya ke takarar gwamnan Edo a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a shekara ta 2016.

Shi kuwa Gwamnan Kano, Ganduje, tuni har ma ya hango nasara ga APC a zaben.

“Dangane da zaben gwamna a jihar Edo, to Jihar Kano na nan yanzu haka tana yin duk abin da za ta iya yi, domin APC ta ci zaben gwamnan Edo. Saboda an bi duk wata hanyar da ta dace. Zabe kam, APC ce za ta yi nasara a jihar Edo.” Cewar gwamna Ganduje.

Next Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Archives

Welcome Back!

Login to your account below

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.