Jam’iyyar PDP ta musanta rade-radin da ake na cewa gwamna Obaseki ya koma Jam’iyyar biyo bayan rasin samun tikitin tsayawa takarar fidda a gwani a Jam’iyyar APC.
Wannan ya fito daga bakin shugaban Jam’iyyar PDP ja jihar Edo ne Mista Tony Aziegbemi a yayin tattaunawa a cikin shirin ‘The Weekend Show’ na tashar talabijin ta AIT.
Tsohon dan majalisar wakilan jihar kuma shugaban Jam’iyyar PDP na jihar a yanzu ya bayyana cewa har yanzu gwamnan bai dawo Jam’iyyar tasu ba.
“A yanzu haka da muke maganar nan gwaman Obaseki bai dawo Jam’iyyar PDP ba”.
Ya kara da cewa Jam’iyyarsu zata yi maraba da gwamnan idan har yanke hukuncin dawowa Jam’iyyar tasu ta PDP.
Shugaban Jam’iyyar ya kara da cewa ko da ya dawo Jam’iyyar ba zai shiga zaben fidda gwani da Jam’iyyar zata yi, sai dai idan shugabancin uwar Jam’iyyar na kasa ne ya bashi dama.
Har wa yau, ya kara da cewa ko da kuwa an bashi damar tsayawa zaben fidda gwani ba zai samu tikiti kai tsaye ba sai ya gwabza da sauran ‘yan takarkaru sannan kuma a ga abinda hali zai yi.
Wannan tada kura dai da ake yi ya biyo bayan hana shi gwamnan jihar ta Edo Mista Godwin Obaseki tsayawa takarar zaben fidda gwani da kwamitin tantancewa na Jam’iyyar APC suka masa, wanda hakan ya bar baya da kura, wasu na ganin cewa shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Adams Oshiomhole shi ne yayi uwa yayi makarbiya wajen ganin Jam’iyyar ta tsayar da dan takararsa.