Jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Tinubu, ya ɓara kan taƙaddamar siyasar dake faruwa tsakanin Jibrin Kofa da masu ruwa da tsaki a Mazabarsa.
Abdulmumin Jibrin ya sanar da cewa ya shirya barin jam’iyyar APC, duk da cewa bai bayyana dalilan da ya san shi barin jam’iyyar ba.
Kazalika bai bayyana jam’iyyar da ya koma ko zai koma ba, sai dai ya ce zai sanar da inda zai koma kafin awanni 24, farawa daga jiya Asabar.
Akwai dai rikici tsakanin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Abdulmumin Kofa tsawon lokaci, wanda ake ganin hakan kila shi ya sanya shi daukar matakin sallama jam’iyyar.
Tuni dai Tinubu ya tuntubi Gwamna Ganduje kan wannan batu da nufin samar da masalaha a shugabancin jam’iyyar da kuma mabobi.
Kafin nan tuni ya gana da Abdulmumin Kofa domin shawo kansa, kuma yayi nasarar hakan, domin kuwa wannan taƙaddamar na dab da zuwa karshe.
Yanzu haka dai Jibrin Kofa zai hadu da Tinubu domin ganawar sirri, biyo bayan matsala da ya samu daga shugabancin karamar hukumar sa, da kuma Gwamna Ganduje.