A wani kokari da jiga-jigan jam’iyyar APC ke yi na sulhu tsakanin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau.
Wata majiya mai karfi tace jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu a jiya Asabar da daddare wajen karfe 12 na dare ya turo da jirgin sama, don d’aukar Shekarau zuwa birnin tarayya na Abuja, domin yi maslaha tsakaninsa da Ganduje, wanda tuni yana birnin Abuja.
Kazalika, majiyar tace a yau Lahadi ne, ake sa ran Shekarau zai dawo birnin Kano, a dai-dai karfe 12 na rana.
Idan za a iya tunawa, a cikin makon nan mai karewa ne, tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya yi watsi da gayyatar da Ganduje yayi masa na ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari a birnin Abuja.
Tun da farko dai, Shekarau ya amince da gayyatar, amma da ya gano ba shugaban kasa ne ke kiran nasu ba, sai yayi watsi da ita.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Ganduje ke kokarin hana Shekarau ‘din komawa Jam’iyyar NNPP.