Mutane sun cika da mamaki bayan bayyanar bidiyon wata kyakkyawar budurwa da ta auri wani saurayi gurgu.
Bidiyon wanda wani mai amfani da sunan @theclements2020 ya sanya a TikTok, ya nuna cewa ma’auratan biyu anyi musu baiko ne a shekarar 2021 bayan sun kamu da ƙaunar junan su.
KU KARANTA KUMA: An cafke wani ɗalibi ɗan Najeriya mai safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar waje
Bidiyon ya nuna lokacin da aka yiwa budurwar baiko da saurayin ta wanda gurgu ne yana zaune akan keken guragu. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Yanzu har sun yi aure inda suka haifi santaleliyar ɗiya mace. An kuma nuna yarinyar a cikin bidiyon lokacin da iyayenta suke mata wasa ɗauke da murmushi a fuskokin su.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su akan bidiyon, inda wasu suke ta mamakin ta yadda aka yi suka haɗu, wasu kuma sun yi ta musu fatan alheri.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@leratok004 ya rubuta:
“So na gaskiya, ɗiyarku tayi kama da mahaifinta.”
@KIM ya rubuta:
“Ku yi haƙuri, kowane mutum a duniyar nan zai samu mai ƙaunar sa.”
Batyah .Y ta rubuta:
“Kowane mutum ya cancanci ya samu ƙauna.”
@followmefeet ta rubuta:
“Gwanin ban sha’awa! Haka so na gaskiya yake. Allah ya albarkace ku da samun shekaru masu yawa cikin farin ciki.”
@Julie ta tambaya:
“Wai ta yaya kuka haɗu? Masoyan asali”
@Felix Nelly241 ya rubuta:
“Ban taɓa yarda da so ba, amma bayan na ganku na tabbatar da cewa lallai akwai so.”
Baturiya Ta Biyo Mijinta Baƙar Fata Sun Dawo Afrika Da Zama, Sun Rungumi Noma Hannu Bibbiyu
A wani labarin na daban kuma, wata baturiya ta baro ƙasarta ta biyo mijinta baƙar fata zuwa Afrika, sun cigaba da noma.
Wata baturiya wacce ta auri wani ɗan Afrika ta bayyana yadda su duka suka baro Amurka suka dawo Afrika da zama domin tara kuɗaɗe.
Baturiyar ta bayyana cewa sun gina gidansu ne a ƙasar Kenya da tsaɓar kuɗin su.