Wasu masoya sun yi aure inda tsakanin shekarunsu 61 ne kuma duk da haka sun yanke shawarar aure, kuma ta ce ya girmi kakanta, Dailymail ta ruwaito.
Miracle Pogue, mai shekaru 24, ‘yar Starkville, Mississippi’s ta hadu da Charles Pogue mai shekaru 75 lokacin tana aiki a wani asibiti a shekarar 2019, nan da nan soyayya ta kullu.
KUY KARANTA: Tsohon shugaban BUK ya rasu
Yanzu haka suna fatan samun haihuwa kasancewar har yanzu Charles bai taba haihuwa ba. Tsohon mai sana’ar sayar da gidajen, Charles ya gabatar da soyyarsa ga ma’aikaciyar jinya bayan sun hadu inda ya nemi aurenta a Fabrairun 2020.
Miracle ta ce shekarun mahaifiyarta 45, kuma kakanta Joe Brown shekarunsa 72, kuma sun nuna amincewarsu kan soyayyar bayan ganin yadda suke soyayya.
Saidai dakyar mahaifinta Kareem Philips mai shekaru 47 dakyar ya amince. Ya ce idan ya je asibitinsu ba ya yarda wani ya taba shi sai ita.
Ranar da ya zo ya ajiye mata wata takarda wacce ya nemi ta rubuta masa lambar wayarta. Daga nan soyayya ta yi nisa har su dan fita wurin shakatawa tare.
Tirƙashi: Bidiyon Tsohon Da Ya Kwashe Shekara 65 Bai Yi Barci Ba Ya Janyo Cece-Kuce
Bidiyon mutumin ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda yayi iƙirarin cewa rabon shi da barci tun shekarar 1962. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Mutumin mai suna Thai Ngoc ya bayyana cewa tsawon shekara 65 bai ko runtsa ba domin samun barci.