Rundunar Sojin Najeriya ta jaddada kudirinta na gudanar da bincike da ci gaba don magance kalubalen tsaro da ke addabar al’ummar kasar yadda ya kamata.
Mejo janaral Abdulsalam Ibrahim, Shugaban Horaswa (Sojoji) ya sake nanata hakan a wajen bude taron bincike da ci gaba na shekarar 2022 da daidaita tsarin karatu ga Makarantun Sojojin Najeriya a ranar Litinin din nan a Abuja.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Rundunar horar da sojoji ta Najeriya (TRADOC) ce ta shirya shirin.
Ibrahim, wanda Mejo janaral Oluyemi Olatoye, mataimakin babban jami’in horaswa ya wkilta, ya ce rundunar ta yi amfani da bincike da kuma ci gaba domin inganta ayyukanta.
Ya ce taron zai dinke barakar da ake samu a harkar bincike da ci gaban rundunar sojojin Najeriya da kuma tsarin karatun ta.
“Saboda haka, ina fatan cewa a zo karshen wannan taron bita, da an cimma manufofin ci gaban sojojin Najeriya.”
Karanta kuma: Sojoji Sun Rusa Jana’izar ‘Yan Boko Haram A Borno, Sun Jefa Bama-bamai A Sansaninsu
A cewarsa, ana sa ran dama irin wadannan za su haifar da ingantattun shawarwari don cike gibin da ke cikin rundunar.
“Hakika na yi farin ciki da cewa rundunar TRADOC ta Najeriya ta himmatu wajen yin aiki mai ma’ana tare da masu ruwa da tsaki wajen inganta ma’aikatanmu, musamman a fannin horarwa, bincike da ci gaba, da kuma daidaita tsarinmu.
“Ina kuma fatan cewa ayyukan da suka dace a nan za su haifar da shawarwari masu dacewa waɗanda za su shirya yadda ya kamata da kuma sanya rundunar sojojin Najeriya don magance matsalolin zamani,” in ji shi.
Ibrahim ya yabawa rundunar TRADOC bisa yin aiki daidai da hangen nesan babban hafsan sojin kasa, Laftanar janaral Faruk Yahaya, na samun “Kwararren Sojan Najeriya a shirye yake don Cimma ayyukan da aka sa a gaba a cikin Haɗin gwiwar Tsaron Najeriya.”
Tun da farko, Mejo janaral Steven Olabanji, Kwamandan TRADOC, ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da samun sauye-sauye a yanayin kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a wannan zamani.
Kwamandan wanda babban jami’in horaswa na TRADOC, Mejo janlar JAL Jimoh ya wakilata, ya ce sauye-sauyen da aka samu sun bayyana a fannonin, da dabaraun ma’aikata, kayan aiki da kayayyaki suransu.
A cewarsa, don tinkarar kalubalen, ya kamata a rika gudanar da bincike da kuma ci gaba a fannin horo da koyarwa.
“Ayyukan bincike da ci gaba sun sake ƙirƙira ko taimakawa don ƙirƙirar dabarun aiki da hanyoyin dabaru, gyare-gyaren kayan aiki, tsarin koyarwa, dabaru da sauransu.
“Shahararrun ma’aikatanmu sun dage sosai wajen tafiyar da al’amuransu daban-daban na shirin kuma ina kira ga dukkan mahalarta taron da su nuna sha’awarsu da kuma cin gajiyar wadannan damammaki.
“A matsayina na mai horar da sojojin Najeriya, na yi imani da cewa za ku fadada ilimin ku don inganta na sojojin Najeriya ta makarantunku daban-daban,” in ji shi.
Kamfanin illancin labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, shirin na kwanaki biyu ya samu halartar manyan hafsoshi daga makarantun soji da cibiyoyin horaswa. (NAN)
A wani labarin kuma: Da Dumi-Duminsa: Kwamishinan Legas Ya Yi Murabus Bayan Rushewar Ginin Oniru
Kwamishinan tsare-tsare da raya birane na jihar Legas, Idris Salako ya yi murabus.
Gbenga Omotoso, kwamishinan yada labarai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin din nan.