Sojoji a Burkina Faso a ranar Litinin din nan sun sanar ta gidan talabijin na kasar cewa, sun kwace mulki a kasar da ke yammacin Afirka, biyo bayan wani bore kan yadda shugaban farar hula ya kasa shawo kan ‘yan tawaye masu ikirarin jihadi.
Wani karamin jami’i ya sanar da dakatar da kundin tsarin mulkin kasar, da rusa gwamnati da majalisar dokokin kasar, da kuma rufe iyakokin kasar daga tsakar daren jiya Litinin, in ji wata sanarwa mai dauke da sa hannun Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba.
Ya ce sabuwar rundunar Patriotic Movement for Preservation and Restoration (MPSR) za ta sake kafa “tsarin mulki” a cikin “lokaci mai ma’ana”, ya kara da cewa za a aiwatar da dokar hana fita na dare a fadin kasar.
Daruruwan mutane ne suka taru don murnar juyin mulkin da sojoji suka yi a Ouagadougou, inda suka yi maraba da sojoji, tare da daga tutar kasar.
Da sanyin safiyar litinin, manyan kasashen Afirka da na yammacin Turai suka yi tir da abin da suka kira “yunkurin juyin mulki” kuma kungiyar EU ta bukaci a gaggauta sakin shugaba Roch Marc Christian Kabore.
Amurka ta kuma yi kira da a saki Kabore sannan ta bukaci “mambobin jami’an tsaro da su mutunta kundin tsarin mulkin Burkina Faso da shugabancin farar hula.”
A cikin wata sanarwa da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya fitar, ya ce “yana matukar yin Allah wadai da duk wani yunkurin kwace gwamnati da karfin makamai”, yana mai cewa abubuwan da suka faru a matsayin “juyin mulki”.
Bayan rahotanni masu cin karo da juna kan halin da Kabore yake ciki, babban jami’in kula da harkokin waje na EU Josep Borrell ya ce a cikin wata sanarwa: “Yanzu mun san cewa shugaba Kabore na karkashin ikon sojoji.”
Ya kira lamarin “abun damuwa matuka”.