Shugaban Rundunar Tsaro ta Ƙasa Janar Lucky Irabor, ya ƙarya ta wani rahoto dake nuna cewa ƴan ta’adda na gina sansani a wuraren Babban birnin tarayya Abuja.
Ƙungiyar Ƙabilar Yarbawa ta Afenifere a ranar Laraba ta koka, inda tace ta samu wasu bayanan sirri daga wata majiya cewa ƴan ta’adda na gina sansani a wuraren Babban birnin tarayya Abuja da Jahar Niger, inda suka buƙaci a ɗauki matakin gaggawa.
Dayake maida martani, Irabo a lokacin taron kwamitin Shugaban ƙasa akan sadarwa a Villa Abuja, a ranar Alhamis, yace rahoton ƙaryane babu ƙamshin gaskiya a cikin shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kano: Gwamna Ganduje Ya Jagoranci Gina Kasuwar Zinare A Garin Batakaye
Ya ɓukaci Al’umma dasu jefar da wannan rahoton, inda ya ƙara dacewa al’umma na ƙirƙirar waɗannan bayanai domin wani ƙudiri nasu.
“Idan har akwai wannan abu da wasu ke koka wa akanshi, Sojoji zasu sani”, inji shi.
Dayake jawabi akan dalilin da yasa sojoji sojoji suka zaɓi kai samame a yankin Kudu maso Gabas, a yayinda ƴan bindiga ke cigaba da musguna wa mutane a Arewa, Rundunar Tsaro ta gano cewa matsalar tsaro ta bambanta tsakanin wani wuri ya zuwa wani wuri.
“Abunda ka samu a kudu maso gabas yasha bamban da abun da ka samu a Arewa,” inji shi.