Sojojin Nijeriya sun bada sanarwar cafke wadansu Kwamandojin Boko Haram 10 a dajin kauyen Bitta a cikin Karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno. An damke su a lokacin da su ke kokarin arcewa daga wutar da sojoji suka rika sanya musu.
Kakakin sojojin a bakin daga, Aminu Iliyasu ne bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar wa manema labarai a yau Asabar a Abuja.
Jaridar Premium Times ta labarto cewa; an damke su ne a ranar 9 Ga Oktoba, a lokacin da sojojin aikin musamman na Birgade ta 26 suka kai wani farmaki a kan su. Iliyasu ya ce da yawan wadanda aka kama an gano cewa su ne suka tuka motocin yakin da suka kai wa garin Gwoza hari cikin 2014.
Sannan ya ce cikin wadanda aka kama din sun hada da Shettima Mustapha Umar, Abba Buji, Alhaji Bukar Madu, wato KAHID, wanda shi mukaminsa a cikin Kwamandojin Boko Haram, yake daidai da Birgediya Janar. Sai kuma Ali Hassan, wanda limamin Boko Haram ne, akwai kuma Alkali Laminu.
Sauran sun hada da Bukur Mustapha, Buba Umaru (wai shi Black Uhuru) kuma ‘Birgediya Janar’ ne, wato KAHID, sai Madu Nosobe, Mustapha Hussaine da Umar Jeddum, dukkan su ‘yan cikin Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno.
Daga cikin wadanda sojojin suka kama, akwai Alhaji Bukar Modu, wanda suka ce sunansa ne na 89 a jerin wasu rikakkun hatsabiban ‘yan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.