Sojoji sun cafke Yan Bokoharam da manyam makamai da miyagun kwayoyi
Rundunar sojojin 195 tare da Rundunar HADIN KAI gami da Jami’an CJTF sunyi nasarar cafke mayakan Bokoharam guda biyu, sun kwace muggan kwayoyi gami da manyan Makamai da suke dauke da shi a yankin Muna dake Borno.
Daga cikin kayayyaki da Aka kwace daga hannun su sun hada da: Kayan gashewa, gatura, mashin, keke guda biyar, wayoyi biyu da Mai nayin abinci da kuma Mai wanda ake sanyawa injin mota.
KARANTA:-Matsalar Tsaro: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe Makarantu 13
Mai magana da yawun sojojin Onyema Nwachukwu, yace “sojojin sun nasarar karbe maganin dake sa karfin maza, maganin bera, maganin kwari da kayan abinci duk suna daga cikin kayayyaki da aka kwace daga wajan Yan ta’addan.”
Sojojin lokacin da suke rangadi cikin mazaunin Yan ta’addan basu bar ko da allura ba, sun kuma rusa gine-ginen da Yan ta’addan ke fakewa.
Manjo Faruk Yahaya ya yabama sojojin kan irin gagarumar nasarar da suka samu, ya kuma umarce su da su maida hankali kada su barma Yan ta’addan koda allura.
Allah yasa mudace