Hedikwatar tsaro ta sojojin Nijeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP guda biyar a ranar Juma’a a Jihar Borno.
Wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran rundunar, Benard Onyeuko, ya fitar ta ce dakarunsu sun fafata da ‘yan bindigar a garuruwan Garal da Bulankesa, inda suka kashe mayaƙa biyu sannan wasu suka tsere da raunuka.
A dai ranar Juma’ar, an yi wata fafatawar a yankin Ashigashiya, abin da ya yi sanadiyyar kashe wasu mayaƙan ƙungiyar biyu sannan aka ƙwace kayayyakin abinci daga sansaninsu tare da lalata shi.
Kazalika, sojoji sun kashe wani ɗan Boko Haram a yankin Doksa, inda suka ƙwato bindigar AK-47 ɗaya da wayar salula biyu da kuma katin shaidar Boko Haram.
A yau Lahadi ne aka yi jana’izar wasu manoma 43 da ‘yan Boko Haram ɗin suka yi wa yankan rago a gonakinsu da ke Zabarmari ta jihar Borno.