Dakarun runduna ta 3 ta sojojin Najeriya karkashin jagorancin kwamandan Birgediya Janar Sinyinah Nicodemus sun kwashe shara daga magudanun ruwa dake kan titin Igbo dake unguwar Sabon Gari a karamar hukumar Fagge a jihar.
Wannan hobbasar dai wani bangare ne na sauke hakkin jama’a na rundunar sojojin Najeriya ga al’ummomin da suke makotaka da su kuma wani bangare na bikin ranar sojoji.
Da yake jawabi yayin taron Birgediya Janar Siniyah Nikodemus ya ce runduna ta 3 sun zabi yankin da za su gudanar da aikin kwashe sharar ne saboda dimbin sharar da aka jibge a yankin wanda ke da illa ga lafiyar jama’a.
Ya yi nuni da cewa, wannan matakin zai aike da sako ga al’ummar wannan yanki domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu ta hanyar kiyaye tsaftar al’ummarsu.
“Muna yin hakan ne ga al’ummar wannan yanki a matsayin wani bangare na ayyukan da muke da su na zamantakewa, mun fara bikin ranar sojoji da sallar juma’a, kuma yau 2 ga watan Yuli ce ranar da muke bikin ranar sojoji, wannan aiki shi ne bikin ranar sojoji na bana”.
Kwamandan ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da gudanar da ayyukansu ta hanyar tsaftace muhallinsu, da nufin inganta lafiyar jama’a.
Salisu Mohammed da Gloria Daniel mazauna unguwar Sabon gari ne, sun yaba da jajircewar da sojojin Najeriya suka yi na yin hakan, inda suka jaddada cewa aikin zai yi matukar tasiri wajen inganta lafiyar dan Adam, kuma zai dakile yaduwar cututtuka masu yaduwa.
Dakarun Sojojin Najeriya wadanda ke da hazaka ne suka fara aikin kwashe sharar da sanyin safiyar yau.