Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama a kewayen babbar unguwar tollgate a karamar hukumar Chikun ta jihar.
Kwamishinan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce daga cikin ‘yan bindigar da sojojin suka kashe, akwai Musti, wanda ya jagoranci wani mummunan hari a shekarar da ta gabata a Kwalejin horas da sojoji ta Najeriya dake Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kama Mamu Ta’addanci Ne Gumi Ya Caccaki DSS
Ya ce Musti ne ya jagoranci harin wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an soji biyu na cibiyar, Laftanar Kwamanda Wulah da Laftanar Okoronkwo, yayin da wani Manjo Christopher Datong ya bace bayan harin da sanyin safiyar ranar 24 ga watan Agustan shekarar 2021.
Kwamishinan yace wani dan bindiga da ya yi kaurin suna mai suna Boderi Isiya, ya tsallake rijiya da baya, inda ya kara da cewa an samu gawarwaki da makamai a wurin, yayin da wasu daga cikin ‘yan ta’addan suka mutu sakamakon harbin bindiga.
Aruwan, ya kasa fitar da alkaluman ‘yan ta’addan da sojojin suka kashe.
Kwamishinan ya ce, “Shahararren dan fashin nan Boderi Isiya ya tsallake rijiya da baya, yayin da sojojin Najeriya suka bindige babban kwamandan sa na biyu tare da wasu mayaka da dama.”
“Hukumomin tsaro sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna wannan ci gaban a cikin wata sanarwa da ta fitar.”
“Binciken da aka yi da sahihan majiyoyin leken asiri na dan Adam ya kara tabbatar da cewa Boderi da kungiyarsa ta ‘yan ta’adda sun yi mummunar rana a hannun dakarun da ke shirye-shiryen yaki.”
“A cewar rahotanni, sojojin sun yi artabu da ‘yan bindigar a kusa da babban yankin Tollgate na karamar hukumar Chikun. ‘Yan ta’addan sun afka cikin ja da baya, sai dai suka ci karo da wani harin kwantan bauna da sojojin suka yi a yankin Sabon Gida.”
“Sojojin sun kai wa ‘yan bindigar mumunan hari, kuma daga karshe suka fatattake su.”
“Mutumin Boderi na biyu, Musti, yana daga cikin wadanda aka tantance, tare da Mai-Madrid Yellow guda daya da Dan-Katsinawa guda daya, da sauran wadanda har yanzu ba a tantance ba. Wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun gamu da raunukan a fafatwar da ke barazana ga rayuwarsu.”
“Musti da Boderi ne ke da alhakin tabarbarewar tsaro a makarantar horas da sojoji ta Najeriya da ke Kaduna, da kuma yin garkuwa da daliban Kwalejin Injiniya ta Tarayya, Sarkin Bungudu da wasu ‘yan kasa da dama a bara.”
Kwamishinan ya kara da cewa wannan farmakin ya burge gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, wanda aka rawaito ya yabawa dakarun da ke karkashin jagorancin babban kwamandan runduna daya ta Kaduna, Manjo Janar Taoreed Lagbaja.
A wani labarin kuma, IPOB Ba Za Ta Iya Yiwa Buhari Wata Barazana Ba — Gwamnatin Imo
Gabanin ziyarar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai jihar Imo a ranar Talata, gwamnatin jihar a ranar Asabar ta yi watsi da barazanar da masu fafutukar kafa kasar Biafra suka yi.
A wani taron manema labarai a Owerri a ranar Asabar, kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar, Declan Emelumba, ya ce kungiyar IPOB ba za ta iya yi wa shugaban barazana ba.