Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun kashe ‘yan bindiga da dama tare da kubutar da wasu mutane 10 da aka yi garkuwa da su a daure a wani sansani a wani samame da suka kai maboyar masu garkuwa da mutane a kananan hukumomin Chikun da Igabi a jihar Kaduna.
An tattaro cewa sojojin sun share sansanoni a tsaunin Apewohe, Dakwala da Kunai a karamar hukumar Chikun.
KARANTA WANNAN LABARIN: DSS: Mun Kama Mamu Ne A Hanyarsa Ta Zuwa Ganawar sirri Da Kwamandojin ‘Yan Ta’adda A Saudiyya
Kwamishinan tsaro na cikin gida da kuma harkokin cikin gida Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an sake balle wani sansani a wani wuri da ke ‘Daban Lawal Kwalba’ a karamar hukumar Igabi, bayan da sojojin suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga da ke gadin mutanen da suka yi garkuwa dasu.
“Sojojin bayan sun fatattaki ‘yan bindigar sun kai farmaki maboyar tare da ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su da aka daure su da sarka. Sojojin sun kwance mutanen da aka yi garkuwa da su,” inji shi
A cewar Aruwan, sojojin sun yi nasarar kwashe mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa wani sansanin soji inda ake kula da lafiyarsu kafin su sake haduwa da iyalansu.
Ya ce gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i, ya yaba wa dakarun da suka gudanar da aikin tare da karfafa musu gwiwa da su ci gaba da kokarinsu.
A wani labarin kuma, Yajin Aikin ASUU: Muna Bukatar Ministan Ilimi Ya Gagguta Yin Murabus—– Kungiyar NANS
Kungiyar daliban Najeriya ta kasa a ranar Talatar da ta gabata ta yi kira ga ministan ilimi Mista Adamu Adamu ya yi murabus saboda yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ke cigaba da yi
Shugaban na NANS ya bayyana haka ne a yayin zanga-zangar da ta gudana a kan titin Legas zuwa Ibadan bisa zargin cewa ministan bai nuna sha’awar tattaunawa da kungiyar ASUU don janye yajin aikin ba.