Hedikwatar rundunar sojin Nijeriya ta fitar da cewa rundunar Operation Lafiya Dole da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta hallaka mayakan Boko Haram kusan 11 a cikin mako guda da ya gabata.
Rundunar ta wallafa hakan ne a shafinta na Twitter, inda ta ce sun yi nasarar hakan ne bayan artabu da suka yi da ‘yan kungiyar Boko Haram din a lokuta daban-daban, inda su kuma a janibinsu suka rasa soja daya sannan daya ya ji rauni.
Rahotanni sun bayyana cewa an kai hare-haren ne a Jihar Borno, a cewar rundunar. Sannan ta kara da cewa wasu mayakan kungiyar biyu sun mika wuya tare da kwato makamai da babura da aka yi wa fentin kakin sojoji.
Kazalika ta ce ta karbi wasu sabbin ‘yan gudun hijira 19 a sansaninta daga kauyen Jebe.