Rundunar soja ta ce ta kashe ‘yan fashi 17 a gari uku da ke cikin Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da John Enenche, Kakakin Hedikwatar rundunar Soja da ke Abuja ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce sun kai harin ne a ranar Alhamis bisa haɗin gwiwar rundunoninta na musamman irin su Gama Aiki da Thunder Strike.
Samamen ya yi sanadiyyar kashe ‘yan fashi 17 kamar yadda suka tabbatar, sannan wasu suka tsere da raunuka a garuruwan Galbi da Damba da Kabarasha da Gwagwada dukkaninsu a Ƙaramar Hukumar Chikun.