Rahotanni sun bayyana cewa dakarun runduna ta 21 na Amored Brigade dake garin Bama sun kashe mayakan Boko Haram guda shida a wani sumame da suka kai a wata haramtacciyar kasuwa da ‘yan ta’addan suka kafa a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
An rawaito cewa harin ya faru ne a yau Larabar da misalin karfe 11 na safe lokacin da sojojin tare da hadin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (CJTF) suka kai farmaki kan haramtacciyar kasuwar da aka fi sani da Kasuwar Daula a kauyen Bararam a garin Bama.
KARANTA ANAN: A Karon Farko Osibanjo Ya Bayyana A Taron FEC, Tun Bayan Yi Masa Tiyata A Legas
A cewar Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ‘yan tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ana ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci a lokacin da sojojin suka farwa kasuwar mai ci ba bisa ka’ida ba.
Ya ce da ganin sojojin sai ‘yan ta’addan suka bude wuta amma cikin gaggawa suka shiga tsakani, inda ya kara da cewa suma sojojin sai suka kara kaimi.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan kasuwar na sayar da kayayyaki irinsu Masara, wake, gishiri, Maggi, mayafi da kayan maye da kuma man fetur ga ‘yan ta’addan, domin musayar karafa.
An ce an garzaya da wadanda ake zargin zuwa hedikwatar da ke Bama domin gudanar da bincike.
A wani labarin kuma:
SSANU, NASU Reshen UNILAG Na Zanga Zangar Adawa Da Janye Yajin Aikinsu