Hedkwatar tsaro a ranar Alhamis ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun Hallaka mayakan Boko Haram/ISWAP sama da 120 a yankin Arewa maso Gabas a cikin makonni uku da suka gabata.
Darakta, Ayyukan Yada Labarai na Ma’aikatan Tsaro ta kasa, Maj.-Gen. Benard Onyeuko ne ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, inda ya ce an kashe kwamandojin ISWAP da dama da wasu hare hare da suka Kai kan mayakan na bama-bamai, da jiragen sama da na kasa.
Ya kuma ce ya zuwa yanzu, ‘yan ta’adda 965 da ‘yan uwansu sun mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban. inda ya ce baya ga ‘yan kungiyar ISWAP 104 da suka mika wuya a baya-bayan nan, an kubutar da mutane 25 da aka yi garkuwa da su.
Kazalika ya ce an tattara bayanan ‘yan ta’addan da suka mika wuya tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar matakin da ya dace.
Da aka nemi jin ta bakin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum na cewa idan aka bar kungiyar ISWAP ta bunkasa, rikicin Boko Haram zai zama wasan yara, Onyeuko ya ce gwamnan ya bayyana ra’ayinsa ne kawai kamar kowane dan Najeriya kuma kowa ya lura da hakan.