Rundunar sojin hadin gwiwa a yankin Arewa maso Gabas mai taken ‘Operation Hadinkai’ ta ce ta kashe ‘yan ta’adda 60, tare da cafke sama da 120 da ake zargin masu tada kayar baya ne a farmakin da suka kai a baya-bayan nan.
Rundunar ta kuma ce ta kubutar da wasu ‘yan matan Chibok uku da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati ta Chibok, dake jihar Borno.
Kwamandan rundunaar na Operation Hadinkai, Manjo Janar Christopher Musa, ne ya bayyana hakan a jiya yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar dake Maiduguri.
“Abin da muke da niyyar yi a matsayin wani bangare na kokarin mu na kai samame shine mu hana su ikon samun dabaru wanda zai hanasu ci gaba da kai farmaki. A yayin aiwatar da murkushe ‘yan ta’addan sojoji sun kara kaimi wajen kakkabe mayakansu.
“Misalin shi ne kama wani Haruna Fulani da Umaru a ranar 13 ga Yuli 2022, wadanda ake zargi da kai wa kwamandan ‘yan ta’addan kayan aiki, Aliyu Ngolde, a yankin Mandara tsaunin Gwoza. Kayayyakin da aka kwato sun hada da dauren kayan mata guda 13, yadi 20 na bakar auduga, rigar mata da takalman roba guda 25 da dai sauransu.”
KARANTA WANNAN LABARIN: An tsaurara jami’an tsaro a kwayar birnin Kano, tare da rufe wasu hanyoyi
Ya ce sojojin sun ceto ‘yan matan Chibok uku a tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 25 ga watan Yuli. Wadanda aka ceto a cewarsa sun hada da Ruth Bitrus da Karuna Luka da yaro da kuma Hannatu Musa da ‘ya’ya biyu.
Idan dai za a iya tunawa, kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da dalibai mata 276 masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno a watan Afrilun shekarar 2014.