Sojoji sun rabama Mutane sama da dubu biyu Magunguna kyauta
Kimanin Mutane dubu biyu mazauna Nasarawan Rashi da kauyukan su, a Gusau Jahar Zamfara suka sami tallafin Magunguna wanda Sojoji suka raba.
Wannan aikin na daya daga cikin ayyukan da suke gabatarwa na ranar murnar jaruman sojoji.
KARANTA:-Yan sanda 5,000 ne tare da Sojoji suke Yaki a Arewa
Manyan Sojojin dake Gusau sunce sun zabi Nasarawan Rashi ne don tallafawa Al’ummar yankin.
Babban Jami’in lafiy na Rundunar sojojin dake Gusau, Hillary Gami cewa yayi Mutanen kauyen suna fama da rashin ruwan sha da Asibitin da sauran kayan more rayuwa.
Yace ” Mun zabe sune saboda sune makoftanmu na kurkusa.
Ya kuma nuna jindadinsa kan irin hadin kan da Yan Kauyen ke badawa wajan zuwa karbar Magungunan.
Tsofaffi, Maza, Mata, Yara da masu ciki ne suka sami wannan tallafin na Magunguna kyauta.
An basu Magunguna na ciwon hawan jini, ciwon siga, ciwon zazzabin cizon sauro, ciwon taifot da na ciwon hakori.
Comments 1