Sojojin Operation Whirl Stroke (OPWS) sun kashe ‘yan bindiga uku a wani samame da suka kai wasu sassan karamar hukumar Kastina-Ala a jihar Benue.
Sabon kwamandan rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS), Manjo-Janar Kevin Aligbe, ne ya bayyana hakan a karshen mako.
“A ranar Laraba ne aka tarwatsa sansanin ‘yan bindiga a Arewacin Katsina Ala inda aka kashe ‘yan bindiga 3 tare da kona sansaninsu. Babu wani barna da aka samu,” kamar yadda ya shaida wa jaridar Daily Trust.
Aligbe, wanda ya hau mukamin kwamandan rundunar OPWS da ke da aiki a jihohi Benue, Nasarawa da Taraba bayan rasuwar magabacinsa, Birgediya Janar Clement Dayo Apere, ya jaddada cewa kalubalen tsaro a kasar nan na bukatar gudunmawar kowa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fararan Hula sun Tsere yayin da ISWAP Suka Farmaki Sojoji a Borno
Tun da farko ya bayyana cewa sojoji kadai ba za su iya magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar ‘yan Najeriya ba yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida a Makurdi babbab birnin jihar.
“Batutuwan da ke tunkaro mu a matsayinmu na al’umma na bukatar kowa ya sa hannu a kai. Sojoji kadai ba za su iya magance matsalolin rashin tsaro ba”
Aligbe ya kara da ba da tabbacin cewa zai ci gaba da samun nasarorin da magabatansa suka samu duk da cewa tawagarsa za ta kara kaimi a dukkanin sassanta na jihohi uku dake aiki.
Comments 1