Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce rundunar sojin kasar ta saki tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram 1,400 sannan aka bar su suka shiga cikin jama’a.
Jaridar PUNCH ta ambato kwamishinan watsa labarai na jihar, Babakura Jato, yana cewa an saki ‘yan Boko Haram din ne kashi-kashi kuma a lokuta daban-daban tun da aka soma shirin ‘Operation Safe Corridor’.
Ya kara da cewa ko da yake tun 2016 aka soma shirin, amma ba a fara sakar ‘yan Boko Haram din ba sai 2018.
Jato ya kara da cewa akasarin mutanen da aka saka ba cikakkun ‘yan Boko Haram ba ne amma ‘yan uwansu ne ko kuma mutanen da aka yi kuskuren kamawa.
“Sau da dama ana sakarsu kashi-kashi. An sake su kashi uku. Kashin farko an sake su ne lokacin Gwamna There have been a series of releases. Shettima, yayin da sauran kashi biyu aka sake su lokacin mulkin Farfesa Zulum”, a cewarsa.