Rundunar sojin Najeriya ta kafa dokar hana fita a garin Askira Uba da kewaye a jihar Borno yayin da sojojin suka dakile wani harin da aka kai a yankin.
A cewar PRNigeria, an ruwaito cewa mayakan na ISWAP sun kaddamar da farmaki a Dilli wanda cikin gaggawa suka dakile sakamakon hadin gwiwar dakarun sojin sama da na kasa.
Dille ƙauye ne a garin Lassa da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Askira Uba.
Wata majiyar leken asiri ta shaidawa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa sojojin Najeriya sun ci gaba da taka-tsan-tsan da kuma shirye-shiryen yaki bayan sun samu bayanai kan motsin ‘yan ta’adda a wasu kauyuka.
“Mun samu bayanan sirrin cewa mayakan na ISWAP sun nufi wata gada ta gabas da kauyukan Wamdeo da Roumirgou a lardin Askira Uba.
“Mun dakile yunkurinsu a yau a wani kauye mai nisa da ake kira Dille da ke karkashin Lassa, Kuma muna shirin tunkarar su,” inji majiyar.
Comments 1