Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 35, Sun Kwato Shanu A Zamfara – Kakakin Soji
Dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe akalla ‘yan fashi 35 a Zamfara a wasu samame biyu da suka yi a jere, in ji sojoji a ranar Litinin.
A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar tsaro, Manjo-Janar John Enenche, an gudanar da ayyukan ne a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce “Bayan bayanan sirri da suka samu game da inda ‘yan fashi da makami suke A wani Sansanin su da ke Ƙaramar Hukumar Bungudu a Zamfara yasa muka kai samame ba tare da ɓata lokaci ba kuma muka yi Naaara, Inji shi.
Dimokuraɗiyya Adon Ƙasa!