Sojoji sun yi wa Ƴan Boko Haram kwanton Ɓauna, sun Hallaka Mayaƙa Bakwai
Dakarun soji na Operation Desert Sanity, da Operation Hadin Kai, ta bayyana cewa sun yi wa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne da aka fi sani da Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād kwanton bauna, inda suka kashe shida daga cikinsu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Ƴan Ƙauye da suka tserewa hare-haren Ƴan bindiga, sun faɗa cikin ruwa
DAILY POST ta tattaro cewa, bayan samun bayanan sirri, dakarun bataliya ta 73, tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force, sun gudanar da wani harin kwantan bauna a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, a kauyen Kayamla dake kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno, wanda ya yi sanadin kashe mayakan.
Wani jami’in leken asiri ya shaidawa Zagazola Makama, wani manazarci kan harkokin tsaro kuma masani kan yaki da ta’addanci a tafkin Chadi cewa ‘yan ta’addan da suka tsere, su ne wadanda ke tserewa daga hare-haren da sojoji ke kai wa a yankunan Boko Haram.
Majiyar ta ce, yawanci suna zuwa yankunan ne domin ta’addanci ga Manoma da kuma sace su a wasu lokutan domin neman kudin fansa.
Ya ce sojojin sun zafafa kai hare-hare kan ‘yan ta’addan, masu hadin gwiwarsu da masu samar da kayan aiki.
A wani labarin kuma: 2023: Ɗan Takarar da zai iya magance Matsalar Tsaro kawai Arewa zata zaɓa
Shugabannin Arewa sun yi alkawarin cewa goyon bayansu a zaben shugaban kasa na 2023 zai kasance ga duk dan takarar da ke da karfin magance matsalar rashin tsaro da kuma ‘yantar da ‘yan Najeriya daga kalubalen da suke fuskanta.
Shugabannin jihohin Arewa 19 da Abuja sun bayyana matsayinsu a wajen wani taro na kwanaki 2 da wata kungiya mai suna Arewa New Agenda (ANA) ta shirya a Abuja.