An Jiyo karar harbe-harbe a safiyar yau Asabar, kusa da fadar Gwamnatin Kasar Guinea dake Conaky babbar birnin Kasar. Biyo bayan wata majiya Mai karfi da ta bayyana cewa, wata fitacciyar rundunar sojojin kasar ne, karkashin jagorancin wani tsohon sojan Faransa, Mamady Doumbouya, ke da alhakin kai farmakin.
Kazalika hotuna da suka fito daga fadar gwamnatin Kasar na nu na cewa, Sojojin kasar sun yi wa Shugaban kasar Mr Alpha Conde juyin Mulki, bayan an hango sojojin zagaye da shi.
An ga Shugaban kasar mai mulkin kama -karya kuma Mai shekaru 83, yana zaune sanye da riga da wando tare da maballan Rogan sa a bude, Wanda yanayin da yake ci, ya nuna bai ji daɗin yanayin ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi garkuwa da Matar Dan Majalissar Dokokin Katsina tare da Yayan shi 2
Idan za’a iya tuna Shugaba Alpha Conde ya lashe zabe karo na uku ne a watan Octoban shekarar da ta gabata, bayan ya sauya kundun tsarin mulkin kasar, domin bashi daman tsaya wa takara, duk da bore da masu zanga-zanga a kasar suka yi.