A ranar Litinin, Rundunar Sojin Ƙasa zata fara gudanar da wani shirin bita na kwanaki uku a faɗin ƙasar.
Taron bitar an yi mashi laƙabi da code named, da Golden Dawn, da Enduring peace gami da Still water a turance.
KARANTA WANNAN LABARIN: “Da ‘Yan Fim da Malamai duk Abu daya ne” inji Salisu Muhammad Officer
A cewar sanarwar data fito a ranar Lahadi daga Daraktan yaɗa labaru na Rundunar Sojin Ƙasa Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, yace Babban Hafsan sojin ƙasa Laftanar-Janar Faruk Yahaya shi zai ƙaddamar da fara gudanar da shirin a jahar Enugu.
Ya ƙara dacewa, shirin kai samamen an tsara shi ne domin magance duk wani irin nau’in ta’addanci, gami da baiwa mutane damar gudanar da rayuwar su.
Onyema ya buƙaci mutane masu makwabtaka da inda ake gudanar da shirin da kada su ji tsoro a lokacin da suke ganin wucewar soji da kayayyakin aikin su.