Hukumomi a Amurka sun ce adadin sojin kasar da suka samu rauni a kwakwalwarsu bayan harin da Iran ta kai sansanin sojinsu da ke Iraq a watan Janairu ya kai 109.
Wadannan alkaluma kari ne mai yawa a kan soji 64 da a baya hukumar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce sun samu rauni sanadiyar harin.
Tun da fari, Shugaba Donald Trump ya ce babu wani dan Amurka da ya ji rauni sakamakon harin.
Harin, wanda aka kai shi ranar takwas ga watan Janairu, ya faru ne sakamakon rikicin da ya barke tsakanin kasashen biyu bayan Amurka ta hallaka kwamandan zaratan sojojin juyin-juya hali na Iran, Qasem Soleimani, a wani harin sama da sojojinta suka kai kan filin jirgin sama na Bagadaza, a Iraq.
Kusan kasha 70 na sojojin da suke sansanin lokacin harin sun koma bakin aiki, in ji wata sanarwa da Pentagon ta fitar.