Majalisar gudanarwar mulkin sojan Guinea ta ce an mayar da hambararren shugaban kasar Alpha Condé zuwa gidan matarsa da ke Conakry babban birnin kasar.
Kwamitin raya kasa na kasar, CNRD, kamar yadda aka fi sani da mulkin soja, ya fada a cikin wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin na kasar cewa, a yanzu Mr Condé yana tare da matarsa, Hadja Djene Kaba Condé.
Kwamitin ta ce, za ta ci gaba da baiwa tsohon shugaban kasar kulawar da ta dace da matsayinsa, kuma hakan ba tare da matsin lamba na kasa, ko na kasa da kasa ba.
Hambararren shugaban mai shekaru 83 ana tsare da shi ba tare da saninsan inda aka boye shi ba, tun bayan hambarar da shi a wani juyin mulki a ranar 5 ga Satumba.
Ya jagoranci Guinea tun lokacin da aka zabe shi a shekara ta 2010, a karon farko da Guinea ta mika mulki ga dimokradiyya.
An dakatar da Guinea daga kungiyar kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS, bayan juyin mulkin.
Kungiyar ta ECOWAS ta kuma sanya takunkumin hana tafiye-tafiye da kuma daskare kadarorin shugabannin da suka yi juyin mulki a Guinea da iyalansu yayin da suke kira da a saki Mr. Condé ba tare da wani sharadi ba.