Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga, sun ƙwato makamai a Imo
Dakarun Birget ta 34 ta Rundunar sojin Najeriya dake Obinze, a Owerri ta Kashe ƴan bindiga guda 4 a Amaifeke da Ihioma dake Ƙaramar Hukumar Orlu ta Imo a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Magance Matsalolin tsaro, Talauci a Arewa —Wata Ƙungiya ga Manyan Arewa
Daraktan Yaɗa Labaru na Rundunar Sojin Nijeriya Onyema Nwachukwu ya bayyana haka a Owerri cewa an ƙwato makaman baya anyi musayar wuta, wanda aka samo bindiga da Harsashi.
Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun ƙunshi Mota ƙirar Hilux a ranar Lahadi aka ƙwato su daga ƴan bindiga da Waya, da kaya tsafi.
Birgediya-Janar Onyeama Nwachukwu yace ƴan bindiga ana kyautata zato ƴan Ƙungiyar Tsagerun Kafa Ƙasar Biafra ne wato IPOB inda aka kashe su a lokacin musayar wutar da Dakarun Soji.
Ya ƙara dacewa an kashe su a lokacin da suke ƙoƙari sanya Dokar Zaman Gida ta hanyar yin harbi ta ko’ina tare da gargaɗin kashe rayuka da Dukiyoyin ƴan Ƙasa.
“Sun buɗe wuta a lokacin da suka hango Dakarun Soji da suke ƙoƙarin ganin an kiyaye rayuka da Dukiyoyin Al’umma.
“Dakarun sun yi musayar wuta dasu, inda suka samu nasarar kashe guda 4 daga cikin su, a yayinda sauran suka tsere,”inji shi.
Mr Nwachukwu yayi kira ga Al’umma dasu riƙa bayar da bayanan sirri akan duk wani motsi na ƴan Ta’adda ga Jami’an tsaro da zaran sun gansu a yankunan su.