Dakarun rundunar Sojiin Nijeriya tare da hadin gwiwar Sojojin hadaka na kasashen da ke makwabtaka da yankin tafkin Chadi, sun yi nasarar dakusar da kaifin kungiyar Boko Haram a wani samame da su ka kai musu a yankin tafkin Chadi.
Kakakin rundunar Sojin, Kanar Sagir Musa ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Sojoji sun kaddamar da samamen ne a sansanin Boko Haram da ke garin Tumbus a yankin tafkin Chadi. Ya kara da cewa sun samu sahihan bayanan da ke nuna cewa, a lokacin da Sojojin suka afka wa ‘yan ta’addan, mayakan su na kan hanyar su ta tserewa ne zuwa yankunan kasashen Sudan da Afirka ta tsakiya don neman mafaka, kuma Sojoji sun kashe manyan kwamandojin su guda bakwai.
Kwamandojin kungiyar da aka kashe kuwa sun hada da Abba Mainok da Bukar Dunokaube da Abu kololo, da Abor Kime da Mann Chari, da Dawoud Abdoulaye da kuma Abu Hamza.
Shugaban -afsoshin rundunar Sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya jinjina wa Sojojin bisa jarumtar da su ka nuna a wannan samame.