Sojojin Nijeriya Sun Sake Ceto Wata Ƴar Makarantar Chibok
Sojojin Najeriya sun ceto wata ɗalibar makarantar Chibok mai suna Ruth Bitrus da aka sace ita da sauran wasu dalibai da dama daga makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati dake Chibok cikin Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilu, 2014.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan bindiga sun hallaka Ƴan Sanda biyu a Enugu
Wani rahoton sirri da Zagazola Makama, masani a fannin yaki da tada kayar baya a yanki tafkin Chadi ya samo daga manyan majiyoyin soji, kuma wakilin jaridar Leadership ya samu, ya nuna cewa Sojojin Birged 2 ne suka ceto Ruth da danta a Bama dake jihar Borno a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022, bayan ta gudo daga hannun mayakan Boko Haram a yankin karamar hukumar Bama dake cikin jihar.
A yayin da take ba da labarin irin halin da ta shiga, Ruth ta ce ta gudo daga dajin Sambisa ne bayanda yan Boko Haram suka sace su daga makarantarta dake garin Chibok tsawon shekaru ta 8 da suka gabata.
Ta ce bam ne ya kashe mijin ta na yanzu (dan ta’adda) a lokacin da yake kokarin tayar da shi a kan dakarun rundunar Operation Hadin Kai dake yankin Arewa maso Gabas.
Ruth ta kara da cewa har yanzu sauran ‘yan matan makarantar na cen ana tsaro da su a dajin Sambisa.
Ta ce “Na dauki kwanaki uku ina tafiya daga wurin ‘yan ta’addan. Na yo guzurin abinci tare da doko yaro na. Wasu daga cikin ‘yan Boko Haram sun ganni a lokacin da nake tserewa, amma sai na boye daji don gudun kada su kama ni,” inji ta.
Idan dai za a iya tunawa a makonni biyu da suka gabata ne Sojojin suka kubutar da wasu ‘yan matan makarantar Chibok din guda biyu Mary Dauda da Hauwa Joseph, bayan sun tsero daga Gazuwa, hedikwatar kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād da aka fi sani da kungiyar Boko Haram da ke da nisan kilomita 9 zuwa karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Kubutarsu ta biyo bayan gagarumin farmakin da dakarun Operation Hadin Kai suke ci gaba da kaiwa, wanda ya janyo yunwa da rugawar yan ta’addan.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da dalibai mata 276, masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati dake garin Chibok a Jihar Borno a watan Afrilun shekarar 2014.
Sama da guda 100 daga cikin ‘yan matan makarantar ne har yanzu ba a san inda suke ba tsawon shekaru 8 bayan da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su