Sojojin Nijeriya ta yi gagarumin nasarar ceto mutum 34 wadanda aka yi garkuwa da su a jihar ta Binuwe, sannan sun kuma yi nasarar halaka shugaban gungun masu garkuwar kamar yadda sanarwar Hedikwatar tsaron ta sanar.
Tuni aka hada dukkanin waɗanda aka ceto da iyalansu kamar yadda sanarwar ta tabbatar.
Haka zalika sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da kwanson harsashinta guda ɗaya.
Dakarun rundunar musamman ce ta ‘Operation Whil Stroke’ ne suka yi nasarar ceto su a wani hari da suka kai a Ƙaramar Hukumar Logo a ranar 16 ga watan Yulin 2020.